Ba Laifin Tinubu Bane Don Majalisa Ta Ki Sahhalewa El-Rufai Ya Zama Minista, Bagudu

Publish date: 2024-06-09

FCT, Abuja - Ministan kasafin kudi da tsara tattalin arzikin Najeriya, Atiku Bagudu ya ce, ba laifin Shugaba Bola Ahmad Tinubu bane don majalisar kasa ta ki sahhalewa Nasir El-Rufai ya zama minista a gwamnatin nan.

A cewar Bagudu, Tinubu ya cika alkawari wajen mika sunan El-Rufai a jerin ministocinsa da ya nemi majalisar ta tantance don yin aiki tare dashi.

Ya bayyana cewa, majalisar ce ta ga dacewar kin amincewa da El-Rufai tare da tabbatar dashi a matsayin ministan, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Ba laifin Tinubu bane rashin amincewa da Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake tattaunawa da jaridar, ya ce tsarin demokradiyya da kundin tsarin kasar ne ya ba majalisar ikon tantancewa da amincewa da nagartar ministoci.

Ya kara da cewa:

"Shugaban kasa bai da wani katabus a kudin tsarin mulkin kasa ya yi wani abu. Hakan daidai ne? Amma haka aka tsara dokar."

Yadda El-Rufai ya yi kokari a kamfen Tinubu

A lokacin gangamin neman zaben Tinubu, El-Rufai na daga cikin wadanda suka yi ruwa suka yi tsaki wajen tattabar da nasarar jam'iyyar APC a zaben 2023.

Kafin zaben, Tinubu ya bayyana rokonsa ga El-Rufai a idon duniya, inda yace yana sha'awar aiki dashi idan ya zama shugaban kasa.

A watan Agustan bara ne aka mika sunan El-Rufai cikin jerin ministoci, amma majalisa ta ki amincewa da shi a matsayin wadanda za su yi aiki da Tinubu.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

Babu wata matsala tsakanin El-Rufai da Tinubu

A bangare guda, jigon jam'iyyar APC a jihar Plateau, Podar Yiljwan Johnson ya magantu kan alakar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Nasir El-Rufai.

Johnson ya ce babu wata matsala tsakanin Tinubu da Nasir El-Rufai kamar yadda ake zargi a wasu bangarori.

Sai dai, har yanzu Shugaba Tinubu ko El-Rufai babu wanda ya bayyana alakar da ake da ita a tsakanin juna.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn56gZRmmZplnJa2p7XNZquipqWXwm6uwKecZpyfo3qurcmao6KrkWLBonnKomSsmZidrq2x1ppknqRdp8KnrchmsJplqpa6onnMoqWiq6SWeqOtxq6brmc%3D