Cikakken Jerin Kasashe 6 da Suka Sauya Taken Kasarsu Ba da Dadewa ba

Publish date: 2024-06-13

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A ranar Laraba, 29 ga watan Mayun 2024, Shugaba Bola Tinubu, ya rattaɓa hannu kan kuɗirin da ya maye gurbin tsohon taken Najeriya na “Arise, O Compatriots" da "Nigeria, We Hail Thee".

An fara amfani da tsohon taken na "Arise, O Compatriots" ne tun shekarar 1978 lokacin mulkin soja na tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Bayan Najeriya akwai wasu ƙasashen nahiyar Afrika da suka taɓa sauya taken da suke amfani da shi a ƙasashensu

Yadda aka sauya taken Najeriya

Majalisar wakilai ta zartar da dokar taken ƙasa ta 2024 a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, inji rahoton jaridar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'adda 140, sun kwato makamai masu yawa

Ƴan majalisar dai sun bayyana cewa taken na "Arise, O Compatriot" ya fito ne daga wata doka ta sojoji.

Hakan ya sanya aka sake dawo da "Nigeria, We Hail Thee" bayan an fara amfani da shi a matsayin taken Najeriya a shekarar 1960.

Ƙasashen da suka sauya takensu kwanan nan

Jaridar Vanguard ta jero ƙasashen da ba su daɗe da sauya taken ƙasarsu ba ta hanyar yi masa kwaskwarima.

1. Australia

A ranar 1 ga watan Janairun 2021 ƙasar Australia ta yi wa takenta na "Advance Australia Fair" kwakwarima.

An sauya wani layi na taken ƙasar daga “For we are young and free” zuwa “For we are one and free".

2. Austria

A shekarar 2012, ƙasar Austria ta sake gyara takenta na “Land der Berge, Land am Strome” domin damawa da kowane jinsi.

Daga cikin taken na baya wanda a ciki akwai inda ake cewa "great sons,” an sauya shi zuwa “great daughters and sons.”

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan bindiga sun kashe ɗan majalisar yanki da shugaban matasa

An yiwa taken wannan kwaskwarimar ne domin tabbatar da cewa taken ya tafi da kowane ɗan ƙasar Austria ba tare da la'akari da jinsinsa ba.

3. Canada

Ƙasar Canada ta yi muhimmin sauyi a cikin takenta na “O Canada,” a cikin shekarar 2018.

A cikin taken an sauya inda ake cewa “in all thy sons command” zuwa “in all of us command".

Sauyin da aka yiwa taken na daga cikin ƙoƙarin da ake yi domin ganin an mayar da taken ya ƙunshi dukkanin ƴan ƙasar ba tare da la'akari da jinsinsu ba.

4. Afirika ta Kudu

A shekarar 1997, Afirka ta Kudu ta sauya takenta domin murnar shiga zamanin mulkin dimokuradiyya bayan mulkin wariyar launin fata da aka yi a ƙasar

An haɗa taken "Nkosi Sikelel' iAfrika" da "Die Stem van Suid-Afrika" domin samar da sabon take a ƙasar.

A cikin ƴan shekarun da suka gabata, an yiwa taken sauye-sauye domin tabbatar da cewa ya ƙunshi dukkanin yarukan ƙasar.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwan da suka faru a majalisar dattawa a makon da ya gabata

5. New Zealand

A shekarar 1977, gwamnatin ƙasar New Zealand ta sanar da cewa taken ƙasar zai kasance "God Save The Queen" da "God Defend New Zealand".

Daga wannan lokacin dukkanin waƙoƙin guda biyu sun samu matsayi matsayi guda ɗaya.

Bayan hawan Sarki Charles III kan sarauta a watan Satumban 2022, an sauya taken na farko zuwa "God Save The King".

Majalisa ta sauya taken Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da ƙudirin dawo da tsohon taken Najeriya domin ƙara kishin ƙasa.

Majalisar dattawan ta amince da ƙudirin wanda Tahir Monguno daga Borno ya gabatar bayan ya tsallake karatu na uku a ranar Talata 28 ga watan Mayun 2024.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboJ3hJRmmqKjkaC4prqMo5yroZ5iuKK%2FwKyfnqZdlrOqvsikmGackWLAtrfAZqqaramWeqyt0pqprK1f