Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa

Publish date: 2024-06-16

Allah yayi wa Maigirma Wazirin Hadejia, Alh. Hashim Amar rasuwa.

Rahoton da Legit ta samu daga shafin Masarautun Arewa yace za'ayi Janaiza karfe 1.30 na rana a kofar Masallachin Mai martaba Sarkin Hadejia.

Daya daga cikin 'yan uwan mamacin, Jamilu Isyaku, ya bayyana cewa Wazirin ya rasu ne da daren Laraba bayan gajeruwar rashin lafiya.

Jamilu ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Yace:

"Ina mai sana da mutuwar baffana Alha Hashim Amar (wanda akafi sani da Wazirin Hadejia) bayan gajeriyar rashin lafiya da daren jiya."

Kara karanta wannan

Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin

"Allah ya azurtashi da Jannatun Frdausi."

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlkaYJ5gJBmm5pllKq6qrrSmmSapJyWtW7FwGawoq%2BRYsSixsiroKdlnZbAor7Arquaql2drqWxyaKYZqqRqMK4rY4%3D