Dalilin da Ya Sa Murja Kunya Ta Ci Gaba da Hawa TikTok Duk da Umarnin Kotu

Publish date: 2024-06-09

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A baya-bayan nan dai labarin dawowar Murja Kunya kan TikTok ya karade kafofin sada zumunta, inda har lauyoyin da suka tsaya mata suka yi martani.

Idan ba a manta ba, mun fada maku cewa, daga cikin sharudan da kotu ta bayar na ba da belin Murja Kunya akwai alkawarin ba za ta kara hawa soshiyal midiya ba.

Kara karanta wannan

'Banex Plaza': Soja ya shararawa wata mata mari har ta fada doguwar suma

Murja Kunya ta jefa lauyoyi a matsala

Dawowar Murja kan TikToka ya sa lauyoyin na ta suka nuna nadamar tsaya mata da suka yi har ta samu beli amma daga karshe ta bijirewa umarnin kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a zantawar Murja Kunya da kafar labaran DCL Hausa, ta ce sai da ta tuntubi lauyoyi suka ba da izini kafin ta ta ci gaba da hawa dandalin TikTok.

"Dalilin komawa TikTok" - Murja

Da aka tambayi Murja dalilin karya umrnin kotun, sai cewa ta yi:

"A lokacin da za a ba da beli na, an ce ranar 16 ga watan da ya wuce zan iya ci gaba da hawa soshiyal midiya, amma da ranar ta zo aka ce in bari sai 16 ga wannan watan da muke ciki."Da na ga ranar ta zo, na kira lauyoyi na a waya, su ka sanar da ni cewa zan iya ci gaba da hawa soshiyal midiya, amma in kiyaye wasu abubuwan da zan rika dora.

Kara karanta wannan

Jarumar BBNaija kuma ƴar kasuwa ta bayyana yadda ta samu N1.3trn tana barci

"Domin gudun wata matsala, na bar Kano, na tafi inda zan ci gaba da dora bidiyoyi na a shafuka na, amma bisa ka'idar zan kiyaye abin da zan rika dorawa."

Saurari tattaunawar a nan kasa:

'Yar TikTok ta maka iyayenta a kotu

A wani labarin, mun ruwaito yadda wata 'yar TikTko da ta ci ta koshi, ta maka iyayenta a gaban kotu bisa tuhumarsu da haifo ta ba tare da sun nemi izininta ba.

Shahararriyar ‘yar TikTok din, Kass Theaz ta na so kotu ta dauki mataki kan iyayen saboda sun haife ta alhalin ba su ji ra'ayinta ko tana so ta zama 'yarsu ko akasin hakan ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC51K2Yp51fZoJ6f5RubGackaG2rbXNZpuaZamWerStjKasq6KRYri2utiaZK2ZXZi2brPAm5hmnJFitaLDwGaroqOkpLhw