Dan Majalisar PDP Ya Nemi Tinubu Ya Fara Tafiye Tafiye a Mota Ko Ya Hau Jirgin Haya

Publish date: 2024-06-28

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - 'Dan majalisar wakilai, Ali Isa, ya ce ya kamata shugaba Bola Tinubu ya fara yin tafiye-tafiye a mota ko kuma ya yi amfani da jirgin haya wajen gudanar da ayyukan gwamnati.

'Dan majalisa yana so a komawa mota

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Isa, wanda shi ne karamin mai tsawatarwa a zauren majalisar wakila daga mazabar Balanga/Billiri na jihar Gombe, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan majalisar na magana ne kan kudirin da shugaban kwamitin majalisar kan harkokin tsaro, Satomi Ahmed ya gabatar kan bukatar a binciki jiragen shugaban kasa.

Jiragen gwamnati na ba da matsala

A kwanakin baya ne dai rahotanni suka ce Tinubu ya yi amfani da jirgin da aka yi hayarsa daga kasar Netherlands zuwa Saudiyya bayan da jirgin gwamnati ya samu matsala.

A farkon wannan wata, mun ruwaito mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya soke tafiyarsa zuwa Amurka, sakamakon wata matsala da jirgin shugaban kasar ta samu.

A lokacin Shettima zai wakilci Tinubu ne a taron kasuwancin Amurka da Afirka na 2024, wanda dole aka tura ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar.

Kara karanta wannan

'An ba ni kudi in sa hannu a tsige gwamnan jiharmu', tsohon kakakin majalisa

"Tinubu ya fara tafiye-tafiye a mota" - Isa

Hon. Isa ya ce ya kamata shugaban kasa da mataimakinsa su rika yin tafiye-tafiye a mota ko kuma su rika hawa jiragen sama na 'yan kasuwa a lokacin da za su gudanar da ayyukansu.

“Mai girma shugaban majalisa, tun da an taso da wani batu, zan ba da shawara cewa shugaban kasa ya dakatar da amfani da jirgin gwamnati; ya koma hawan na 'yan kasuwa.“Hakazalika, wata hanyar da za ta taimaki ‘yan Najeriya ita ce idan shugaban kasar yana yin tafiye-tafiye a mota. Wannan zai ba 'yan kasar yakinin gwamnati za ta gyara tituna."

Hon. Kalu ya yi wa Hon. Isa martani

Sai dai, jaridar Daily Trust ta ruwaito mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu wanda ya jagoranci zaman ya ce bai kamata shugaban kasa ya rika tafiye-tafiye a mota ba.

"Shin kana nufin cewa, shugaban kasa, mai girma na daya a Najeriya ya rika yin tafiye-tafiye a mota?"

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

-Hon. Kalu ya tambayi Hon. Isa.

Hon. Isa ya jaddada bakansa na cewa Tinubu zai iya amfani da jirgin haya idan ma ba zai iya yin tafiye-tafiye a mota ba.

Tinubu ya hana sayo motocin fetur

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya hana mukarrabansa, hukumomi, ma'aikatu da dukkanin jami'an gwamnati sayo motoci masu amfani da fetur.

Shugaba Tinubu ya kuma ba da umarnin fara sayo motoci da janareta masu amfani gas din CNG domin rage kashe kudade a wajen sayen fetur da dizal.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn93hJFmo5qkkZiyuK3RZqGiqpeeeq6t05qhmqSZqK5uwMBmpZ6lmWLBqrrUm6xmsZFis6K%2BwGarmp6ZrrJuwMCfoLKdXZZ6rrvTmmSkp12ftrOzyKdkoZmplnw%3D