Emefiele: Tsohon Gwamnan CBN Ya Fara Girbar Abin da Ya Shuka Wajen Canjin Kui

Publish date: 2024-06-03

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan kudi N300m.

Kotun ta amince da belin Emefiele ne bayan gurfanar da shi a gabanta kan tuhume-tuhume shida da suka shafi buga sababbin takardun Naira ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta bada belin Emefiele bayan ya ki amincewa da laifi

Tsohon gwamnan CBN shi ne kaɗai wanda ake tuhuma a ƙarar wadda ke gaban mai shari'a Maryanne Anenih a babbar kotun tarayya da ke Maitama, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emefiele ya musanta tuhumar da ake masa

Emefiele ya musanta laifin da ake tuhumarsa da su wanda hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta shigar kuma aka karanta a zaman kotun.

Sauran sharuddan belin sun hada da cewa ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa wadanda kowannensu ya mallaki kadarori a yankin Maitama a Abuja.

Mai shari’a Anenih ta umarci wanda ake kara da ya miƙa takardun tafiye-tafiyensa ga kotu kuma kada ya sa ƙafa ya fita kasar nan ba tare da izinin kotu ba.

Sharuɗɗan belin Godwin Emefiele

Alkaliyar ta amince da sharuddan beli makamancin wannan wanda mai shari’a Hamza Muazu, wani alkalin babbar kotun Abuja, ya gindaya wa Emefiele lokacin da aka gurfanar da shi a gabansa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na tunanin kwashe kuɗin ƴan fansho ta yi wasu muhimman ayyuka

Mai shari’a Anenih ta buƙaci Emefiele ya miƙa takardun shari'a (CTCs) na takardun da ya mika domin cika belin da mai shari’a Muazu ya bayar a baya.

Daga nan kuma sai ta ɗage zaman zuwa ranar 28 ga watan Mayu, 2024 domin shiga cikin shari'ar gadan-gadan, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

DSS ta kai samame harabar kotu

A wani rahoton kun ji cewa jami'an DSS sun kutsa kai cikin kotu ana cikin shari'a, sun tafi da mutum biyu da ake tuhuma a jihar Ogun ranar Talata.

Lamarin dai wanda ya keta doka ya haifar da hayaniya a harabar kotun, inda lauyan waɗanda ake tuhuma ya caccaki DSS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbn92fpBmq6ynmKS7brPWmqSnmZ5isKO6jJ6knp6ZmrmmediaZKyZnap6o7HLomSkmZ5iwba01KaYq2WSqrSiedKamZuhnmK4trWO