Jerin Hadurran Jiragen Sojojin Najeriya 4 Da Suka Faru a Shekarar 2023 Tare Da Dalilai

Publish date: 2024-06-20

A shekarar 2023 da ke dab da ƙarewa, jiragen sojojin Najeriya da dama sun gamu da ibtila'in hatsari a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Na baya-bayan nan shi ne jirgin rundunar sojin sama wanda ya faɗo yayin da ya fita Operation ɗin yaƙi da barayin ɗanyen man fetur a jihar Ribas, ɗaya daga cikin jihohin yankin Neja Delta.

Sai dai kamar yadda rahoton jaridar Aminiya ya tattaro, matuƙan jirgin da sauran sojojin da ke ciki sun tsira da rayuwarsu a haɗarin wanda ya auku ranar Jumu'a.

Mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya tabbatar da aukuwar hatsarin inda ya ce babu wanda ya mutu daga cikin sojojin da ke cikin jirgin.

Ya ce hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar, ya garzaya wurin domin "gane wa idonsa da kuma ganin halin da sojojin ke ciki."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Rayukan mutum 16 sun salwanta, wasu mutum 27 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin haɗurran jirgin da suka auku a 2023

A wannan shafin, Legit Hausa ta tattaro muku jiragen sojojin da suka yi hatsari tare da ranar da ibtila'in ya faru a wannan shekara da ke shirin ƙarewa.

1. Hatsarin jirgin soji a Legas

A ranar 9 ga watan Fabrairu, 2023 jirgin sojin Najeriya da ke aikin kula da teku ya yi hatsari a jihar Legas.

Bayanai sun nuna cewa jirgin kirar Cessna Citation CJ3 ya faɗo ƙasa ne sakamakon rashin lafiyayyun tayoyi. Babu wanda ya mutu.

2. Hatsarin da ya auku a Makurdi

Watanni da dama bayan faruwar haka ne, jirgin rundunar sojin sama kirar FT-7NI ya yi haɗari a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.

Sai dai bisa sa'a matuƙan jirgin waɗanda ke ɗaukar horo sun tsira ra rayuwarsu a hatsarin wanda ya auku ranar 14 ga watan Yuli, 2023.

Kara karanta wannan

Harin bam kan masu Mauludi: CDS ya nemi afuwar yan Najeriya, ya yi muhimmin alkawari 1

3. Jirgin helikwafta a Neja

A watan Augusta, 2023, jirgi mai saukar angulu mai lambar ƙira MI-171 ya gamu da haɗari yayin da yaje ɗauko gawarwakin sojoji da waɗanda suka jikkata a Neja.

Jirgin helikwaftan ya faɗo ne a ƙauyen Chukuba na jihar Neja ranar 14 ga watan Agusta.

4. Wanda ya faru a Fatakwal

Na karshe, shi ne hatsarin jirgin sojojin da aka wayi gari da shi a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas jiya 1 ga watan Disamba, 2023, rahoton Arise TV.

Jirgin wanda ke aikin yaƙi da ɓarayin ɗanyen mai, ya gamu da haɗari ne da misalin ƙarfe 7:45 na safiyar Jumu'a. Har yanzu ba a faɗi abinda ya haddasa hatsarin ba.

An Kashe Gawurtaccen Ɗan Bindiga

A wani rahoton na daban Jami'an tsaro yan banga sun halaka ƙasurgumin ɗan garkuwa da mutane, Dogo Oro, a jihar Kebbi ranar Jumu'a.

Sakataren watsa labaran Kauran Gwandu, Ahmed Idris, ya ce ɗan ta'addan ya jima yana takura wa al'umma a kananan hukumomi biyu.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlla4N3hY9moZ6qmaN6qa3DrqmrmZ5it6q%2BwKCcp2WjpLewtsinZKeZmpq%2FqsXAZpuaZaOquKJ5xZqprmWRYsCpscqaqZqqXWd9c3%2BO