Tsohon Sanata Kuma Dattijon asa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Jihar Kano
- Najeriya ta yi babban rashi yayin da sanata a jamhuriya ta biyu, Sidi Ali, ya riga mu gidan gaskiya a ranar Alhamis da yamma
- Marigayi, mahaifin muƙaddashiyar kakakin CBN ta ƙasa, Hakama Sidi Ali, ya rasu ne yana da shekaru 96 a duniya
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi ta'aziyyar rasuwar dattijon ƙasar a madadin gwamnati da al'ummar jihar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Tsohon sanata a jamhuriya ta biyu kuma gogaggen dan jarida, Sidi Ali, ya rasu da yammacin ranar Alhamis yana da shekaru 86 a jihar Kano.
Ɗaya daga cikin iyalan tsohon sanatan ne ya tabbatar da haka ga wakilin jaridar Punch ranar Jumu'a, 26 ga watan Afrilu, 2024.
![](https://cdn.statically.io/img/netstorage-legit.akamaized.net/images/f072a7b30e38972f.png)
Kara karanta wannan
Kwanakin PDP za su zo karshe, tsohon ɗan Majalisar Tarayya ya sake ficewa
![](https://cdn.statically.io/img/netstorage-legit.akamaized.net/images/f072a7b30e38972f.png)
Marigayi Sidi Ali, shi ne mahaifin daraktar sashin sadarwa ta riko a babban bankin Najeriya (CBN), Hakama Sidi Ali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattijon ƙasa marigayi Ali ya yi aiki a cibiyar yan jarida ta Najeriya, ma'aikatar yada labarai da hukumar yada labarai ta ƙasa.
A matsayinsa na dan siyasa mai daraja, ya kasance 'dan jam'iyyar APC kuma ya taka rawar gani a kwamitin dattawan jam'iyyar na jihar Kano.
Gwamnan Kano ya yi ta'aziyya
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya yi ta'aziyyar wannan rashi ga iyalan marigayin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Jumu'a.
"Na samu labarin rasuwar Alhaji Sidi Ali, a yammacin ranar Alhamis, ya rasu yana da shekaru 86 a duniya."Fitaccen dan siyasar ya kasance amintaccen Jami’in Hulda da Jama’a wanda ya yi aiki tukuru don tabbatar da labaran gaskiya a lokacin yakin basasar Najeriya.![](https://cdn.statically.io/img/netstorage-legit.akamaized.net/images/36da192a78bd7f68.jpg)
Kara karanta wannan
APC: Ana tangal tangal da kujerarsa, Ganduje ya fadi wadanda za su iya gyara Najeriya
"Ba za a manta da shi ba bisa gudummuwar da ya bayar a matsayin sanatan jamhuriya ta biyu. A madadin gwamnati da al'umma Kano, ina mika ta'aziyyata ga iyalansa. Allah ya sa Jannatul Firdaus ta zama makwancinsa."- Gwamna Abba Kabir.
Gwamnatin Kano ta fara bincike
A wani rahoton kuma Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta fara binciken dalilan yawaitar mutuwa da ake samu a yan kwanakin nan a kauyuka da biranen jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a Kano, inda ya shawarci al'umma.
Asali: Legit.ng
ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllbYZ3g49mq6ynmKS7br%2FAp5itmV2otqW1jJqjomWplnqzrdKuZLKZnpZ6pa2MrJ%2Beo5Gnwm6ElWaYZqKZna6zecqapahn