Wata mata ta saka hoton ta cikin hotunan auran Zahra Buhari

Publish date: 2024-06-16

- Hotunan wata mata yar arewa a cikin hotunan auran Zahra Buhari yayi zagaye yanar gizo cikin sauri

- Matar wacce ta so kasancewa a bikin amma bata samu katin ya gayyata ba don haka ta yi amfani da fasaha

- A cikin hotunan, cikin hikima ta shuka kanta cikin hotunan auransu da taimakaon photo shop kuma ya kasance abun ban dariya.

Bikin yar shuaban kasar ya cika da manyan masu fada a ji a kasar. Ba wai kowa bane zai iya samun katin ayyata cikin sauki kamar yadda shugaban kasa ya so auran ya kasance a saukake.

Ga wadanda suka so kasancewa a gurin taron bikin don taya ma’auratan farin ciki, ya karya masu zuciya saboda basu samu damar kasancewa da Zahra ba a wannan rana ta musamman.

Don haka ne wannan matashiya ta yi amfani da damarta. Ya nuna karara cewa ta so kasancewa a gurin bikin don hakan ne ya kai ta ga amfanifasaharta gurin hada hotonta cikin hotunan ma’auratan da yayi fice. Kalli hotunan a kasa:

Don haka, wanene zai ce bata halarci bikin ba? Bayan tana da hujja na kasancewa a gefensu.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9j3Bva3FlYsSiwMBmpJqskWLBonnSmqKaZZikwbC6jK2YZpuZoLaveceoq66mkaN6osHRmqVmspGdv6J5wa6fmqqZY7W1ucs%3D