Zabe: Ku zabi shugaba mai gaskiya da rikon amana - Sheikh Bala Lau

Publish date: 2024-06-12

- Fitaccen malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci al’umman Najeriya da su duba Mutum mai gaskiya da rikon amana su zabe shi a matsayin shugaban kasa

- Bala Lau ya shawarci Jama'a su guji dukkanin shugaba wanda yayi kaurin suna ta fuskar cin amana da rashin gaskiya

- Shugaban Izalan ya kuma bukaci Hukumar Zabe ta kasa da cewar, tubalin zaman lafiyar kasa yana a hannun su ne, cewa su ji tsoron Allah a lamuransu

Fitaccen malamin nan na addinin Musulunci kuma Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus Sunnah na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bukaci al’umman Najeriya da su duba Mutum mai gaskiya da rikon amana su zabe shi a matsayin Shugaban Kasa, a babban zaben da za a gudanar a watan gobe.

Sheikh Bala Lau ya jadadda cewa babban abinda ake nema a Shugabanci shine gaskiya da rikon amana a wajen Shugaba, dukkanin Shugaban da aka san shi da kamanta gaskiya da rikon amana shine Shugaban da ya dace Jama'a su zaba, kuma lallai Jama'a su guji dukkanin shugaba wanda yayi kaurin suna ta fuskar cin amana da rashin gaskiya.

Malamin yayi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidanshi da ke Kaduna dangane da batun zabe da ya kunno kai.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Rabon kudin Kamfen ya tada kura tsakanin Ummi Zeezee da wasu manyan yan wasa

Ya kuma yi nasiha ga dukkanin 'yan takara musanman na Shugaban Kasa da cewar su amince da sakamakon zabe da Hukumar zabe zata fadi, domin hakan zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a kasa, da dorewar shi kanshi mulkin na Dimokuradiya.

Shugaban Izalan ya kuma bukaci Hukumar Zabe ta kasa da cewar, tubalin zaman lafiyar kasa yana a hannun su ne, domin sune kadai suke da alhakin sanar da sakamakon zabe, to don Allah kada su amince wani ya saye su da kudi domin su canza sakamakon zabe, su sani cewa amana ce aka basu, kuma Allah zai tambaye su akan wannan amana gobe Kiyama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kWpvbHFoYseirsRmoq5lqpavqnnSoaygmZKWeq6tyGaemqubnsaiecOaZKuhm6S7bq3MmqWaZaOdsqq3x2aZmqSRYrmiwY2hq6ak