Zaben Gwamna: APC Ta Rasa Babban Jigon da Take Ji da Shi, Ya Samu Matsayi a NNPP

Publish date: 2024-06-08

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Barista Olugbenga Edema, ɗaya daga cikin manyan ƴan takarar APC da suka nemi tikitin takarar gwamna a jihar Ondo ya koma New Nigeria People’s Party (NNPP).

Jim kaɗan bayan haka NNPP ta miƙawa Barista Edema tikitin takarar gwamna a zaɓen jihar Ondo da za a yi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

"Yadda Tiinubu yake biyan tallafin fetur bayan sanar da soke tsarin tun ranar farko"

NNPP tayi sabon 'dan takara a Ondo

Edema ya zama ɗan takarar NNPP ne a zaɓen fitar da gwani da jam'iyyar ta shirya a Akure, babban birnin jihar Ondo ranar Laraba, jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shirya zaben ne domin maye gurbin tsohon ɗan takarar gwamna, Ayeni Oluwatosin, wanda ya janye niyyar takara haka kurum.

Barista Edema ya bugi ƙirjin cewa ya shirya kayar da da ɗan takarar APC kuma gwamna mai ci, Lucky Aiyedatiwa idan a akwatun zaɓe.

Meyasa ɗan takarar NNPP ya janye?

A wasiƙar da ya miƙa domin tabbatar da janyewa daga takara, Mista Oluwatosin ya ce ya ɗauki matakin ne domin ɗaga ƙimar NNPP.

“Ni, Ayeni, Oluwatosin Israel, dan takarar gwamna a NNPP a zaben da za a yi ranar 16 ga Nuwamba, 2024 a jihar Ondo, na haƙura da takara.

Kara karanta wannan

Fitaccen basarake kuma tsohon kwamishinan ƴan sanda ya kwanta dama

"Ba don komai na janye daga takara ba sai don ina kishin jam'iyyata NNPP," in ji shi.

NNPP za ta tsaida 'dan takarar gwamna

Haka nan kuma Mista Peter Olagookun, shugaban NNPP na jihar Ondo ya tabbatar da janyewar dan takarar, kamar rahoton Vanguard ya kawo.

Ya ce babu wanda ya tilasta masa, ya janye ne bisa ra'ayin kansa kuma domin ya ba NNPP damar zaƙulo ɗan takarar da zai baiwa maraɗa kunya.

Atiku ya ce tallafin mai ya dawo

A wani rahoton kuma, an ji Atiku Abubakar ya buƙaci shugaban ƙasa ya fito ya faɗawa ƴan Najeriya gaskiya game da biyan tallafin man fetur.

Wazirin Adamawa ya yi ikirarin cewa cire tallafi duk maganar baka ce, inda ya ce kuɗin tallafin bana watau shekarar 2024 ka iya kai wa N5.4trn.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC%2FyLKYrJlfZoJ6go9qa2annpm8bn6Pa2tmnZSauqJ52Jpkn6GTmnqlrcaaZJqok2LGonnZmqSaZZSWu27AwKSYq5miYrS4rcynmKdlnqO9sXs%3D